Image
Shekarar da ka rubuta
2021

Ramadaniyyat 1442 H [2]

Daga Babban Malami, Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo (Hafizahullah).

Dalilin Nasarar Annabi (ﷺ)

1. Allah (SWT) ya sanar da Manzonsa (ﷺ) cewa, shi ne wanda ya karfafe shi da nasararsa da kuma muminai wadanda suka yi imani da shi. Shi Allah, shi ne ya hada tsakanin zukatansu da Musulunci. Da a ce Manzon Allah (ﷺ) zai kashe duk dukiyar da take bayan kasa don ya hada tsakanin zukatansu da ba zai iya ba, to amma ga shi Allah (SWT) ya hada tsakaninsu. Lalle shi mubuwayi ne mai hikima. [Duba, Al-Anfal, aya ta 62 zuwa 63].
2. A kan fadar Allah: (Idan da za ka kashe duk abin da yake bayan kasa gaba daya ba za ka iya hada tsakanin zukatansu ba), Ibn Mas'ud (RA) yana cewa: "Wannan ayar ta sauka ne game da wadanda suke soyayya don Allah". [Albazzar, 2077].
Wannan yana nufin dukkan sahabbai da suka yi imani da shi, watau Muhajiruna da Ansar. [Ibn Adiyya, juzi'i na 2, shafi na 548]. 
3. Babu shakka nasarori da Annabi (ﷺ) ya samu, ya same su ne bayan Allah (SWT) ya karfafe shi da wasu abubuwa da suka taimaka masa.
Daga cikinsu, akwai, taimakon da Allah (SWT) ya yi masa na goya masa baya da ya yi.
Sannan ya kuma hada shi da wasu mataimaka masu gaskiya wadanda suka ba shi gagarumin taimako wanda har ya kai shi ga cin wadannan nasarori. 
4. Wannan shi ne abin da ya bayyana a fadarsa: (Shi ne Wanda Ya karfafe ka da taimakonsa da kuma muminai.) [Al-Anfal 62].
5. Muminan nan da suke tare da Annabi (ﷺ) ba wasu ne ba illa sahabbansa, wadanda su ne tawaga ta farko da ta sami sauraron karatun Alkur’ani daga bakin Annabi (ﷺ) lokacin da ake saukar da shi. Don haka wannan al’umma ta sahabbai su ne wadanda suka fara samun tarbiyar da Allah ya umarci shi (ﷺ) yayin da ya yi wa al'ummarsa, inda yake cewa: (....yana kuma tsarkake su,) [Al-Bakara: aya ta 129].
5. Lalle hadin kai da sahabbai suka samu, ba zai samu ba a tsakaninsu ba don imani da biyayya da suka yi wa Annabi (SAW) ba. Ba don imanin gaskiya da ya cika zukatansu ba, to da ba su sami irin wannan hadin kai ba wanda har Allah da kansa ya yabe su da shi. 
6. Tun kafuwar duniya ba a taba samun wani mai koyarwa kamar Annabi (ﷺ) ba. To wadannan sahabban su ne almajiransa, wadanda suka samu karatu a hannunsa, suka samu tarbiya irin tashi, ya yi ayyuka, suka yi ayyuka irin nasa, suka yi aiki da abin da ya koyar da su. 
7. Wadannan sahabbai su ne wadanda suka yi imani da shi imani na gaskiya, wadanda Allah ya ba da shaida a kansu da cewa: (Wadannan su ne muminai na hakika.) [Al’anfal: 74]
8. Su ne wadanda imani ya ratsa kokon zuciyarsu,  ta yadda babu wani daga cikinsu da yake tunanin ya yi ridda, ko mai irin wahalar da zai sha da irin  kowa ce tsangwama da tsana da zai hadu da ita, hakan ba zai sa shi ya ja da baya ba.