Dr.%20Muhammad%20Sani%20Umar%20Image.jpeg

Suna:

 

Cikakken sunan Malam shi ne Muhammad Sani bn Umar bn Musa Rijiyar Lemo.

 

 

 

Haihuwa


An haife shi a 1st July 1970, a birnin Makka na kasar Saudi Arabiya. Ya yi kuma kuruciyarsa ne a unguwar Rijiyar Lemo da ke birnin Kano, Nijeriya.

Karatu a Matakin Farko


Malam ya yi Firamarensa a makarantar Khairul Bariyya Islamic Primary School da ke Kano (1978-1983). Sannan ya ci gaba da karamar sakandire (H.I.S) a sakandiren Shahuci Kano (1987), kuma ya wuce Makarantar Ilimi mai zurfi ta addinin Musulunci, Gwale, in da ya kammala babbar sakandiren (Senior Islamic Studies) da daraja ta farko (Distinction) a shekarar 1989.

Jami'ar Madina


Dr. Muhammad Sani ya samu gurbin karatu a tsangayar ilmin hadisi ta jamiar musulunci ta Madina in da ya kammala digirinsa na farko a fannin ilimin hadisi da nazarin addinin Musulunci (B.A. in Hadith Science and Islamic Studies,1994) da digirinsa na biyu a fannin ilimin hadisi da nazarin addinin Musulunci (M.A.in Hadith Science and Islamic Studies, 2000) dukkanninsu ya fita da daraja mafi girma (First Class da Distinction). Bisa sha’awarsa ta ilmi mai zurfi da bincike, malam ya zarce da karatun digirinsa na uku (PhD) a jamiar musulunci ta Madina wanda Allah ya ba shi damar kammalawa a shekarar 2005, da daraja mafi girma (Distinction)

Malamai


Malam ya yi karatun litattafai masu yawa a wajen malamai da dama a nan gida Nijeriya da kuma Saudiyya, wadanda suka hadar da:

 • Malam Hamza Adakawa (Akhdari, Arbauna hadisan, Ishriniya, Hamziyya da sauransu)
 • Mal. Sani Inuwa (Nahwu da Sarfu)
 • Mal.Mahbub Abdulkadir Sumaly (Balaga ta Tarjamar)
 • Dr. Bashir Hasan (Adabin Larabci da Tarjama)
 • Mal.Aminu Mahe (Tarihi)

Daga cikin malamansa da ya yi karatu a wajensu a kasar Saudiyya kuwa akwai:-

 • Sheikh Abdulmuhsin Al-Abbad (Tauhid)
 • Sheikh Ali Abdurrahman Alhuzaifi limamin Madina (Tauhid)
 • Dr. Abdulaziz Al-Abdullatif (Jarh Wattaadil)
 • Sheikh Muhammad Matar (Tadwin and Ruwat)
 • Sheikh Dr. Hafiz Alhakami (Musdalahul hadis)
 • Sheikh Dr.Muhammad Nur Saif (Musdalahul hadis)
 • Sheikh Dr.Abdussamad Abid (Musdalahul hadis)
 • Sheikh Dr. Umar Hawiyya (Tafsir)
 • Sheikh Dr. Faihan Almudairi (Fiqh)

Dalibansa

Najeriya

Malam ya fara harkokin koyarwa tun shekarar 1405 A.H/1985 da darasin littafin Fathul Majid sharhin Kitafut-Tauhid na Abdurrahman ibn Hassan Aali Sheikh ga taron talibai da littafin Bugulugul Maram a Unguwar Rijiyar Lemo har Allah ya yi masa tafiya izuwa Jami’ar Musulunci ta Madina.

Kasar Saudiyya

Malam ya koyar da darusa da dama a kasar Saudiyya ciki har da takaitaccen littafin Mihhajjus Sunnah da littafin Risaala na Imam Al- Shafi’ da kuma Littafin Bulugul Maram. Dalibai da dama sun halarci wadannan darusa, mafi shahara daga cikin su

 • Sheikh Nasir Yahaya Jihar – Malami a Aminu Kano School for Shari’a and legal Studies
 • Sheikh Dr. Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu – Federal University Dutse
 • Sheikh Dr. Muhammad Muslim Ibrahim Jihar – Associate Professor Al-Qalam University Katsina
 • Sheikh Alhassan Sa’id Jos
 • Sheikh Muhammad Sani Bala Jos
 • Sheikh Dr. Munir Abdallah Jos
 • Professor AbdulRashid Abdulqaniy – Gombe State University
 • Sheikh Rashid Jos
 • Sheikh Shaakir Jos
 • Sheikh Dr. Abdallah Getso Kano – Sa’adatu Rimi Collage of Education Kano
 • Sheikh Abubakar Abbas Kano yana cikin daliban masu himma
 • Sheikh Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo Kano – Collage of Education Gumel
 • Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi Sani Rijiyar Lemo – Bayero University Kano
 • Sheikh Dr. Abdallah Usman Kano – School of Continue Education, Bayero University Kano
 • Sheikh Dr. Umar Garba Dokaji Gombe
 • Sheikh Dr. Ibrahim Disina Bauchi – MD Sunnah TV
 • Sheikh Yahaya Rabi’u Kura
 • Sheikh Murtala Da’a - Sokoto
 • Sheikh Muhammad Kabiru Maru Zamfara – Director Ibn Uthaimin Islamic Centre Zamfara
 • Sheikh Dr. Muhammad Kabiru Goje Kebbi
 • Sheikh Muhammad Kabiru Salis Katsina
 • Sheikh Muhammad Basiru Kano
 • Sheikh Dr. Shuaibu Jibril Jos
 • Da Sauran Daliban da ambatonsu bai zo ba anan

Wasu daga cikin Rubuce-Rubuce


 1. Dhawabit al-Jarh wat Ta'dil inda Al-Hafiz Az-Zahabi, (M.A thesis, an wallafa a kasar London, U.K 1995)
 2. Bita da tahkikin Littafin Al-Ighrab na Al-Imam An-Nasa'i, wanda aka wallafa a Al-Ma'athir, Madina, K.S.A. a shekarar 1995.
 3.  Bita da tahkikin Littafin At-Tamyiz Fi Talkhis Takhrij Ahdith Sharh Al-Wajeez, na Al-Hafiz Ibn Hajar Al-Athqalaani, wanda aka wallafa by Adhwa' As-Salaf, Riyadh, K.S.A a shekarar 2005.
 4. Makarantar Hadith a garin Makkah da Madinah a karni na farko da na biyu da kuma tasirinta a kan ilimin hadisi. (Wanda aka wallafa cikin harshen larabci) (An buga a Darul Minhaj, Riyadh a shekarar 2005)
 5. Ra’ayoyi biyu masu hannun riga, na Abul Hasan Ali An-Nadwy (an rubuta da harshen Hausa). (Kano, Nigeria 1999). An sa ke bugashi a shekarar 2022
 6. Mahimmancin Sunnah a yaren Hausa. (An rubuta a harshen larabci) (An Wallafa a King Fahd Qur'an Complex, K.S.A.  a shekarar 2004.
 7. Littafin Ayyami Ma’a Daa’iyatil Jeel, An Wallafa a kasar Masar a shekarar  2011. Ya kunshi bayanin rayuwarsa tare da marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam
 8. Littafin Bughyatul Mushtaq Fi Sharhi Risalati Shaikhil Islam Ibn Taimiyya Ila Ahlil Iraq, wanda aka wallafa a kasar Masar a skekarar 2013.
 9. Littafin Nabiyyur-Rahmah, (Sirar Annabi Muhammad S.A.W) (a Wallafa a kasar Masar a shekarar, 2012, 2013 da kuma 2014).
 10. Littafin At-Tabseer Li Majaalisit  Tafseer, (Egypt, 2012, 2013).
 11. Littafin Asheikh Usman bn Fodiye: Qiraa'tun Fee Turathihil Elmi an buga a kasar Masar a shekarar 2015.
 12. Littafin Tamamu Attahfiq Fi Siratus Saddiq, (Tarihin Sayyadina Abubakar AS-Siddiq R.A ) (An buga a Kasar Masar, 2015)
 13. Littafin Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya (An buga a kasar Masar a shekarar, 2015).
 14. Littafin Al Bina’ Al- Ilmi Liddaa’iya (An Buga a kasar Masar a shekarar 2015).
 15. Ithafus Sami' Wal Qari' Fi Khatm Saheehul Bukhari, (An wallafa a Nigeria a shekarar 2018).
 16. Littafin Bughyatul Muhtaj Fee Khatmi Saheehi Muslim bn Al-Haj, (An wallafa a Nigeria a shekarar 2019).
 17. Fayyataccen Bayani Na Ma'anoni Da Shiriyar Al'Kur'ani, (Tafsirin AlQur’ani a harshen Hausa ) (An Buga a Bairut Lebanon 2020).
 18. Littaffin Fatawoyin Rahama (Wanda aka buga a Nigeria a Shekarar 2021
 19. Littafin Ramadaniyyat (Takaitattun rubuce-rubuce da ake gabatarwa a kowace rana a Watan Ramadan ) wanda aka wallafa a Nigeria a Shekarar 2021
 20. Littafin Addibajah Fi hukmi Ta’adudil Masaajid min gairi haajah – Littafin dake jan hankali kan yawaitar Masallatan Juma’a ba tare ta bukata ba (Ba a kai ga buga shi ba zuwa yanzu)

 

Da'awa


 • Babban Malami a sashen addinin musulunci na Jami’ar musulunci ta Alkalam dake Katsina daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2012
 • Babban Malami a sashen addinin musulunci na Jami’ar Bayero dake Kano daga shekarar 2013 zuwa yanzu
 • Shugaban kwamitin daukar sababbin mambobi na hadaddiyar kungiyar malamai ta Afrika
 • Karantarwa a daurar da jami’ar madina take gabatarwa ga malaman Arabiya da darusan addinin Musulunci. (Maiduguri, Kano da Bauchi)
 • Babban Daraktan Cibiyar Fassara da Bincike ta Imamul Bukhari, (Al-Imamul Bukhari Centre For Research and Translation) Kano
 • Limamin Babban Masallacin Juma'a na Dorayi, Kano
 • Shugaban Cibiyar Tattara Karatuttukan Sheikh Ja'afar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre (SJIDC))
 • Shugaban Cibiyar Tarihin Cigaban addinin Musulunci da kuma tattaunawa tsakanin addinai dake Jami’ar Bayero, Kano (Centre For Islamic Civilization and Interfaith Dialogue (CICID))

Wasu daga Mahimman Darusan da Malam ya ke gabatarwa a yanzu

Malam yana gabatarda darusan da dama a garuruwan Kano, Katsina da kuma Bauchi wanda suka hadar da:

  • Darasin Tafsirin Al-Qur’ani a Masallacin Usman Bin Affan, Kano
  • Darusan Tafsirin Al-Qur’ani a watan Ramadan a Masallacin Gwallaga na Jahar Bauchi
  • Darasin Adda'u Waddawa'  a Masallacin Modibbo Jihar Katsina
  • Darasin sharhin littafin Kalimatul Ikhlas a masallacin Kerau dake Jihar Katsina
  • Sharhin Takaitaccen Littafin Sahihul Bukhari duk ranar Asabar a Masallacin Usman bin Affan Gadon Kaya
  • Darasin Littafin Akida duk ranar Litinin a Masallacin Usman Bin Affan Gadon Kaya
  • Darasin sharhin Manzumar Imam Suyudi ta Ilimin Hadisi a Jihar Bauchi
  • Shirin Fatawoyin a gidan Talabijin da Rediyo a Jihohin Kano (Rahama Radio), Kaduna (DITV) da Jigawa (Radio Jigawa)

Wasu daga cikin Tarurrukan duniya da Malam ya halarta


Malam ya halarci tarurrukan karawa juna ilmi da kwasa-kwasai da dama a nan gida Nijeriya da kasashen Saudi Arabiya, Sudan, Mali da sauransu. wanda suka Hadar da

 1. International Conference on Sunnah and Sirah, organized by the Ministry of Islamic Affairs, K.S.A. presented a topic titled (The Importance attached to Sunnah In Hausa Literature) ( Madinah, 2004).
 2. International Conference on Supporting the Holy Prophet (S.A.W), organized by the International University Of Khartum, and Al-Muntada Organization, Al-Khartum, Sudan, presented a topic titled (The Position of the holy Prophet within his companions and the rest of Ummah. (Sudan, 2007).
 3. Bamako Conference For The Importance of the media in Da’awah, which took place on 20th – 24th July, 2010 presented a paper titled (Media participation: Its importance and Criteria).
 4. The regional Conference on Da'awa in Sudan under the theme of "Adda'iya Al-Mutamayyiz" Khartum, 19th - 23rd October 2014, presented a topic titled: "Al-Bina'ul Ilmi Lidda'iya" (i.e. making a solid Academic background for Islamic Preacher".
 5. International Islamic Conference of Security Stability in the Face of Contemporary Challenges organized by Muslim World League with Cooperation of J.I.B.W.I.S Nigeria Held in Abuja Between 16th to 19th March 2016, Presented Paper Titled (Al-Ghuluw: Asbabuhu wa Ilajuhu “Extremism: Factors and Wayout”).
 6. Conference on leadership organized by Al-Muntada Al-Islamiy, Held in Khartoum Sudan between 10th to 14th April 2016, (At-Taurisul Qiyadiy fi Garb Ifriqiyyah: Tajarub wa Tahadiyyat “The Leadership in west Africa: Examples and Challenges”).
 7. The Conference on the Protection of Societies organized the International Union of Muslim Preachers held in Doha Qatar between 2nd to 4th March 2016, Presented Paper Titled (Tahsinul Mujtama’ Minal Makhadir Al-Aqadiyya: At-Tashayyu’ Fi Nigeria “ The Protection of the Society from the Dread Beliefs: Shi’a in Nigeria”).
 8. International Conference on Islamic and Challenges of Development in the 21st Century Organized by Departmrnt of Islamic Studies and Sharian in Collaboration with Centre for  Qur’anic Studies Bayero University Kano Nigeria, Presented Paper Titled (Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya “Secularism and its Impact on the Muslim Societies”).
 9. International Conference on Islam in Africa: Combating Extremism and Terrorism organized by International Moderation Forum in Hashimite kingdom of Jordan, in Cooperation with the Islamic peace Society and the Nigerian Centre for Arabic Research, Paper Presented Titled: “Advancing peace by establishing the Al-Wasatiyya and avoiding the extremism”, Held between 8th to 9th August 2015.

Dr Muhammad Sani, a yanzu haka yana zaune a birnin Kano da iyalinsa in da ya shagaltu da karatuttuka da ayyukan da’awa.