- 59 views
Ramadaniyyat 1442H [3]
1. Hiraklu shi ne Sarkin Rumawa. Ba jimawa da hawansa gadon sarauta, sai ya fara shirye-shiryen yadda zai yaki Farisawa wadanda a baya suka yaki kasarsa suka kuma yi musu ta'adi mai yawa. Hiraklu ya samu galaba a kan abokan gabarsa Farisawa ya ci su da yaki, inda har ya kai birini Mada'inu.
2. Ta bangare guda kuwa yana bibiyar abin da yake faruwa a tsibirin Larabawa, inda ya samu labarin bayyanar Annabi (ﷺ). Tun daga lokacin yake son ya samu gamsasshen bayani game da wannan sabon Annabi da ya bayyyana. Sai kawai ya ji labarin shigowar ayarin fataken Labarawa lardin Sham domin fatauci. Sai ya aika a zo masa da shugabansu.
3. Abu Sufyan shi ne yake shugabantar wadannan fatake. Yayin da aka kawo shi gaban Hiraklu, sai ya fara yi wa Abu Sufyan (RA) tambayoyi game da Manzon Allah (ﷺ), ya kuma shaida masa cewa, lalle ya fada masa gaskiya, idan kuwa ya kuskura ya yi masa karya, to lalle wadanda suke tare da shi su karyata shi.
4. Cikin tambayoyin da ya yi Abu Sufyan akwai tambayarsa cewa: "Shin akan samu wani daga cikin wadanda suka yi imani da Annabi (ﷺ) ya yi ridda ya bar addininsa bayan ya karbe shi?" Sai Abu sufyan ya ce: "A’a". Sai Hiraklu ya ce: “Haka imani yake a duk lokacin da haskensa ya riga ya gauraya da zuciya”. [Bukhari#7 da Muslim#1773].
5. Wannan shaida da Hiraklu ya yi amfani da ita, shaida ce ta tarihi, wacce take nuna cewa dukkan annabawa tare da sahabbansu da suka yi imani da su, kuma suka shaku da su kwarai da gaske, suka yarda da abin da suka zo da shi, to irin wadannan ba sa yin ridda su rabu da addininsu.
6. Hirakilu ya kafa shaida da wannan a kan cewa, lalle Muhammadu (ﷺ) Manzo ne daga Allah (SWT), ba wani mutum ne da ya zo don ya cimma wata bukata ta rayuwar duniya ba.
7. Domin abu ne sannane a tarihi cewa, yana daga cikin halayen wadanda suke haduwa don kawai cimma wata manufa ta duniya, musamman manufa ta siyasa ko ta mulki, yau idan ka gan su tare, to gobe kuma za ka ga sun rabu, watau duk sanda suka isa wata mahada inda masalahohinsu za su raba hanya, wani tasa maslaharsa ta yi gabas, wani kuma tasa ta yi yamma. Kowa daga cikinsu zai nufi inda masalaharsa ta nufa ne ya bar dan'uwansu.
8. Wannan shi ne abin da aka sani a rayuwa ta yau da gobe wadda aka gina ta ba a kan imani da Allah ba.
9. To amma ita haduwar Annabi (ﷺ) da sahabbansa ba haduwa ce ta masalaha zalla ba, duk da cewa Annabi (ﷺ) ya gyara musu rayuwarsu ta duniya, sun tashi daga rayuwar ta-ci-barkatai sun zama masu rayuwa a kan manufa da tsari, to amma ba wannan ne kawai ya hada su ba. Babban abin da ya hada su shi ne, imani da Allah (SWT) shi kadai da bauta masa ba tare da hada shi da komai ba.
10. Wannan shi ne gaskiyar lamari game da sahabban Annabi (ﷺ), gaskiyar da ba za ta taba canjawa ba, tarihi ya tabbatar da ita da hujjoji masu yawan gaske da har ba za su lissafu ba. Yarda da wannan gaskiyar shi ne tsantsar hankali da basira, karyata hakan kuwa, ko kuma sanya shakku da kokwanto a kansa shi ne tsagwaron jahilci da rashin hankali da dagulewar basira.