Image
Rana ta
[4]
Shekarar da ka rubuta
2021

Ramadaniyyat 1442H [4]

1. Irin halin da sahabban Annabi (ﷺ) suka shiga ya kara tabbatar da ingancin imaninsu. Sun jure wa dukkan wahala da tsangwama da tashin hankali da suka sami kansu a ciki, kamar yadda suka yi hakuri da yunwa da kishirwa. Suka hakura da kasuwancinsu, suka hakura da iyalinsu da gidajensu da ‘yan’uwansu, suka yi hijra suka bar kasashensu, suka bi Annabi (ﷺ) garin Madina, don su taimaka masa, saboda sun yi imani da cewa Annabin Allah ne na gaskiya, har aka samu wasu sun rasa rayukansu wurin ba wa Annabi (ﷺ) da abin da ya zo da shi kariya.

2. Allah (SWT) ya tabbatar da haka inda yake cewa:

(Akwai wasu mazaje daga muminai da suka cika abin da suka yi wa Allah alkawari da shi; akwai daga cikinsu wanda ya hadu da ajalinsa, akwai kuma daga cikinsu wanda yake sauraron (ajalinsa); kuma ba su canja (komai na alkawarin da suka yi ba). [Ahzab: 23].

3. Al-Khatib Al-Bagdadi (Ya rasu shekara ta 463H) yana cewa:

"Ko da a ce babu wani nassi daga Allah wanda yake nuna nagartar sahabban Annabi, to da rayuwarsu kadai ta isa ta tabbatar da hakan. Sun hijira sun bar kasashensu, sun yi jihadi don Allah, sun kuma taimaka wa addinsa da Annabinsa (ﷺ). Sun sadaukar da rayuwarsu da dukiyoyinsu, sun rasa iyayensu da 'ya'yansu. Sun yi wa junansu nasiha. Ga su kuma da karfin imani da yakini. Wannan kadai ya isa ya tabbatar da nagartarsu da tsarkinsu. Tabbas sun fi duk wasu da za su zo daga baya don su ba da kyakkyawar shaida a kansu. Wannan shi ne abin da kafatanin malamai masana addini suka yarda da shi wadanda duniya ta yarda da iliminsu da tsantseninsu". [Duba, Al-Khatib, Al-Kifaya, shafi na 48].