Rana ta
[17]
Shekarar da ka rubuta
2019

Da Ambaton Allah Ne Zukata Suke Nutsuwa

1. Koyaushe dan'adam cikin nema da bukata yake. Haka Allah ya halicce shi tun farko. Don haka dole ne ya nemi biyan bukatarsa ko dai a wurin Allah ko kuma a wurin wanin Allah.

2. Dalilin bukatar dan'adam kuwa, shi ne tawaya da kasawa da Allah ya halicce shi da su, don haka dole ne ya nemi taimakon wani wanda zai toshe masa wannan gazawar ya biya masa bukatarsa da ta zame masa dole.

3. Wani abin mamaki a al'amarin dan'adam shi ne, duk yadda ya kai ga nuna kwalafacinsa a kan wani abu na duniya ya matsa lamba wajen nemansa, da zarar ya yi nasarar samunsa, ba da jimawa ba zai ji yana bukatar wani abin daban madadinsa ko kuma yana son kari a kan na farko da ya samu. Wannan ya sanya Manzon Allah (SAW) yake cewa: "Da a ce dan'adam yana da kwazazzabo biyu na zinariya da sai ya nemi karin na uku, babu abin da zai cika wa dan'adam cikinsa sai kasa"[Bukhari#6436 da Muslim#1049].

4. Don haka zuciyar dan'adam kullum cikin kwadayi da bukata take, babu abin da zai gamsar da ita sai samuwar kyakkyawar alaka da Allah (SWT) da saninsa da sanin sunayensa da ayyukansa yadda ya kamata a san shi da samun kusanci da shi da yawan ambatonsa. Ta haka ne zuciyar dan'adam za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali, kamar yadda Allah yake cewa: (Lelle da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa). [Ra'ad, aya ta 28].