Misali [23]

Ramadaniyyat 1442/2021

Hiraklu shi ne Sarkin Rumawa. Ba jimawa da hawansa gadon sarauta, sai ya fara shirye-shiryen yadda zai yaki Farisawa wadanda a baya suka yaki kasarsa suka kuma yi musu ta'adi mai yawa. Hiraklu ya samu galaba a kan abokan gabarsa Farisawa ya ci su da yaki, inda har ya kai birini Mada'inu.

Sahabban Annabi (ﷺ): Kakkyawar Shaida Daga Rayuwarsu

Irin halin da sahabban Annabi (ﷺ) suka shiga ya kara tabbatar da ingancin imaninsu. Sun jure wa dukkan wahala da tsangwama da tashin hankali da suka sami kansu a ciki, kamar yadda suka yi hakuri da yunwa da kishirwa. Suka hakura da kasuwancinsu, suka hakura da iyalinsu da gidajensu da ‘yan’uwansu, suka yi hijra suka bar kasashensu, suka bi Annabi (ﷺ) garin Madina,

Dalilin Nasarar Annabi (ﷺ)

1. Allah (SWT) ya sanar da Manzonsa (ﷺ) cewa, shi ne wanda ya karfafe shi da nasararsa da kuma muminai wadanda suka yi imani da shi. Shi Allah, shi ne ya hada tsakanin zukatansu da Musulunci. Da a ce Manzon Allah (ﷺ) zai kashe duk dukiyar da take bayan kasa don ya hada tsakanin zukatansu da ba zai iya ba, to amma ga shi Allah (SWT) ya hada tsakaninsu. Lalle shi mubuwayi ne mai hikima. [Duba, Al-Anfal, aya ta 62 zuwa 63].

Ramadaniyyat 1442H [1] Annabi (SAW) Da Al'ummarsa: Tsananin Bukata Da Gagarumar Nasara:

1. Allah SWT ya yi wa wannan al’umma baiwar aiko mata da fiyayyen annabawa, a  daidai lokacin da al’ummar Larabawa da sauran al'umman duniya suke cikin fagamniya da dimuwa da rashin sanin makama da alkibla, kamar yadda Allah SWT ya bayyana hakan a cikin [Suratul Ali Imran 164 da Suratul Jumu’a: 2] 
2. Dan'adam ya kasance yana rayuwa a cikin bata mabayyani, duk da cewa kafin a aiko Annabi (ﷺ) akwai sauran burbushin addinin Yahudu da  na Nasara da addinin Annabi Ibrahim (AS), sai dai kuma duk an canja su an jirkita su.