no image
Dr. Muhd Sani Umar R/Lemo

Suna:


Cikakken sunan Malam shi ne Muhammad Sani bn Umar bn Musa Rijiyar Lemo.

Haihuwa


An haife shi a 1st July 1970, a birnin Makka na kasar Saudi Arabia. Yayi kuma kuruciyarsa ne a unguwar ‘yan mata dake birnin Kano, Nijeriya.

Karatu a Matakin Farko


Malam ya yi Firamarensa a makarantar Khairul Bariyya Islamic Primary School dake Kano (1978-1983). Sannan yaci gaba da karamar sakandire (H.I.S) a sakandiren Shahuci Kano (1987), kuma ya wuce Makarantar Ilimi mai zurfi ta addinin Musulunci, Gwale, in da ya kammala babbar sakandiren (Senior Islamic Studies) da daraja ta farko (Distinction) a shekarar 1989.

Jami'ar Madina


Dr. Muhammad Sani ya samu gurbin karatu a tsangayar ilmin hadisi ta jamiar musulunci ta Madina in da ya kammala digirinsa na farko (B.A. in Hadith Science and Islamic Studies,1994) da digirinsa na biyu (M.A.in Hadith Science and Islamic Studies, 2000) dukkanninsu ya fita da daraja mafi girma (First Class da Distinction). Bisa sha’awarsa ta ilmi mai zurfi da bincike, malam ya zarce da karatun digirinsa na uku (PhD) a jamiar musulunci ta Madina wanda Allah ya bashi damar kammalawa a shekarar 2005, da daraja mafi girma (Distinction)

Malamai


Malam yayi karatun litattafai masu yawa a wajen malamai da dama a nan gida Nijeriya da kuma Saudi Arabiya, wadanda suka hadar da:

 • Malam Hamza Adakawa (Akhdari, Arbauna hadisan, Ishriniya, Hamziyya da sauransu)
 • Mal. Sani Inuwa (Nahwu da Sarfu)
 • Mal.Mahbub Abdulkadir Sumaly (Balaga)
 • Mal. Bashir Hasan (Adab)
 • Mal.Aminu Mahe (Tarikh)

Daga cikin malamansa da ya yi karatu a wajensu a kasar Saudiyya kuwa akwai:-

 • Sheikh Abdulmuhsin Al-Abbad (Tauhid)
 • Sheikh Ali Abdurrahman Alhuzaifi limamin Madina (Tauhid)
 • Sheikh Abdulaziz Abdullatif (Jarh Wattaadil)
 • Sheikh Muhammad Matar (Tadwin and Ruwat)
 • Sheikh Dr. Hafiz Alhakami (Musdalahul hadis)
 • Sheikh Dr.Muhammad Nur Saif (Musdalahul hadis)
 • Sheikh Dr.Abdussamad Abid (Musdalahul hadis)
 • Sheikh Dr. Umar Hawiyya (Tafsir)
 • Sheikh Dr. Faihan Almudairi (Fiqh)

Tarurruka


Malam ya halarci tarurrukan karawa juna ilmi da kwasa-kwasai da dama a nan gida Nijeriya da kasashen Saudi Arabiya, Sudan, Mali da sauransu. wanda suka Hadar da

 1. International Conference on Sunnah and Sirah, organized by the Ministry of Islamic Affairs, K.S.A. presented a topic titled (The Importance attached to Sunnah In Hausa Literature) ( Madinah, 2004).
 2. International Conference on Supporting the Holy Prophet (S.A.W), organized by the International University Of Khartum, and Al-Muntada Organization, Al-Khartum, Sudan, presented a topic titled (The Position of the holy Prophet within his companions and the rest of Ummah. (Sudan, 2007).
 3. Bamako Conference For The Importance of the media in Da’awah, which took place on 20th – 24th July, 2010 presented a paper titled (Media participation: Its importance and Criteria).
 4. The regional Conference on Da'awa in Sudan under the theme of "Adda'iya Al-Mutamayyiz" Khartum, 19th - 23rd October 2014, presented a topic titled: "Al-Bina'ul Ilmi Lidda'iya" (i.e. making a solid Academic background for Islamic Preacher".
 5. International Islamic Conference of Security Stability in the Face of Contemporary Challenges organized by Muslim World League with Cooperation of J.I.B.W.I.S Nigeria Held in Abuja Between 16th to 19th March 2016, Presented Paper Titled (Al-Ghuluw: Asbabuhu wa Ilajuhu “Extremism: Factors and Wayout”).
 6. Conference on leadership organized by Al-Muntada Al-Islamiy, Held in Khartoum Sudan between 10th to 14th April 2016, (At-Taurisul Qiyadiy fi Garb Ifriqiyyah: Tajarub wa Tahadiyyat “The Leadership in west Africa: Examples and Challenges”).
 7. The Conference on the Protection of Societies organized the International Union of Muslim Preachers held in Doha Qatar between 2nd to 4th March 2016, Presented Paper Titled (Tahsinul Mujtama’ Minal Makhadir Al-Aqadiyya: At-Tashayyu’ Fi Nigeria “ The Protection of the Society from the Dread Beliefs: Shi’a in Nigeria”).
 8. International Conference on Islamic and  Challenges of Development in the 21st Century Organized by Departmrnt of Islamic Studies and Sharian in Collaboration with Centre for  Qur’anic Studies Bayero University Kano Nigeria, Presented Paper Titled (Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya “Secularism and its Impact on the Muslim Societies”).
 9. International Conference on Islam in Africa: Combating Extremism and Terrorism organized by International Moderation Forum in Hashimite kingdom of Jordan, in Cooperation with the Islamic peace Society and the Nigerian Centre for Arabic Research, Paper Presented Titled: “Advancing peace by establishing the Al-Wasatiyya and avoiding the extremism”, Held between 8th to 9th August 2015.

Rubuce-Rubuce


 1. Dhawabit al-Jarh wat Ta'dil inda Al-Hafiz Az-Zahabi, (The Criteria of Grading and Degrading of Hadith Narrators) (M.A thesis, published in London, U.K 1995)
 2. Editing and authentication of Al-Ighrab by Al-Imam An-Nasa'i, published by Al-Ma'athir, Madina, K.S.A. 1995).
 3.  Editing and authentication of At-Tamyiz Fi Talkhis Takhrij Ahdith Sharh Al-Wajeez, by Al-Hafiz, published by Adhwa' As-Salaf, Riyadh, K.S.A, 2005.
 4. The School of Hadith in Makkah and Madinah During the first and Second Centuries and its Impact on Hadith Sciences. (Written in Arabic) (PhD thesis –Published in Darul Minhaj, Riyadh, 2005).
 5. The Islamic Creed of Ahlusunna Wal Jama'ah by Sheikh Al-Etheimeen (Translation into Hausa) (Published by University of Madina press, K.S.A. 1993).
 6. Two different views between Sunnis and Shi'its, by Abul Hasan Ali An-Nadawy (Translation into Hausa).(Kano, Nigeria 1999).
 7. The Importance attached to Sunnah In Hausa Literature. (Written in Arabic) (Published by King Fahd Qur'an Complex, K.S.A. 2004).
 8. Ayyami Ma’a Daa’iyatil Jeel, My dairy with the Prominent Scholar late Ja’afar Mahmud Adam. (Published, Egypt, 2011).
 9. Bughyatul Mushtaq Fi Sharhi Risalati Shaikhil Islam Ibn Taimiyya Ila Ahlil Iraq, The Commentary notes on the Ibn Taimiyya’s massage to the people of Iraq. (Egypt, 2013).
 10. Nabiyyur-Rahmah, (The authentic biography of the Holly Prophet Muhammad S.A.W) (Egypt, 2012, 2013, 2014).
 11. At-Tabseer Li Majaalisit  Tafseer, (An Academic Criteria of the Qur'anic Interpretation in various schools) (Egypt, 2012, 2013).
 12. Asheikh Usman bn Fodiye: Qiraa'tun Fee Turathihil Elmi (Review on His Academic Works). (Egypt 2015).
 13. Tamamu Attahfiq Fi Siratus Saddiq, The Biography of Abubakar AS-Siddiq R.A ) (Egypt, 2015)
 14. Al Al-maniyyah wa Atharuha fil Mujtama’atul Islamiyya (Secularism and its Impact on the Muslim Societies) ( Egypt, 2015).
 15. Al Bina’ Al- Ilmi Liddaa’iya ( The Edusational Basic of the Muslim Preacher) ( Egypt, 2015).

Da'awa


 • Babban Malami a sashen addinin musulunci na Jami’ar musulunci ta Alkalam dake Katsina daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2012
 • Babban Malami a sashen addinin musulunci na Jami’ar Bayero dake Kano daga shekarar 2013 zuwa yanzu
 • Shugaban sashen sabbin mambobi na hadaddiyar kungiyar malamai ta Afrika
 • Mamba a Hadaddiyar kungiyar malamai ta Afrika, daga shekarar 2016 zuwa yanzu
 • Taron karawa juna sani ga malaman Arabiyya, Jami’ar Musulunic, Madinah, Saudi Arabia. (Maiduguri & Bauchi)
 • Babban Daraktan cibibiyar Fassara da Bincike ta Imamu Bukhari, Kano
 • Limamin Babban Masallacin Juma'a na Dorayi, Kano
 • Shugaban cibiyar Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre (SJIDC)
 • Malam yana gabatarda darusan da dama a garuruwan Kano, Katsina da kuma Bauchi wanda suka hadarda:
  • Darasin Tafsirin Al-Quran a Masallacin Usman Bin Affan, Kano
  • Darasin Adda'u Waddawa'  a Masallacin Modibbo Jihar Katsina
  • Darasin sharhin littafin Kalimatul Ikhlas a masallacin Kerau dake Jihar Katsina
  • Darasin sharhin Manzumar Imam Suyudi ta Ilimin Hadisi a Jihar Bauchi
  • Shirin Fatawoyin Rahama a gidan Talabijin da Rediyo na Rahama

Dr Muhammad Sani, a yanzu haka yana zaune a birnin Kano da iyalinsa in da ya shagaltu da karatuttuka da ayyukan da’awa.