dr

Neman Addu'a

Assalamu Alaikum Warhmatullah.

'Yan'uwana Musulmi,

1. Kasarmu tana cikin matsananciyar bukatar addu'o'inmu, saboda matsalar tsaro da ta ta'azzara, masu son su wargaza wannan Kasa sun fito haikan don cimma burinsu.

2. Al'ummarmu ta Musulmi a fadin Kasarnan suna bukatar addu'a, yadda matsalolinsu kullum suke ta karuwa, ake kwararar da jininsu a ko'ina ake salwantar da dukiyoyinsu, ake raba su da gidajensu da sana'o'insu.

3. Shugabanninmu suna bukatar addu'a, musamman yadda arna da majiya dadinsu suka tashi haikan wajen su ga sun kawar da duk wani mai ruhin addini da kokari wajen taimakon al'umma, daga siyasa da shugabanci a Kasar nan.

4. Mu yi amafani da watan Ramadan mai albarka da muke ciki, mu yi tawassali da ayyukanmu na ibada; azumi, salla, karatun Alkur'ani, sadaka, da sauransu, don Allah ya karbi addu'armu ya tausaya mana, ya kawo mana sauki da zaman lafiya.

Tags

Add new comment

Restricted HTML

  • Allowed HTML tags: <a href hreflang> <em> <strong> <cite> <blockquote cite> <code> <ul type> <ol start type> <li> <dl> <dt> <dd> <h2 id> <h3 id> <h4 id> <h5 id> <h6 id>
  • Lines and paragraphs break automatically.
  • Web page addresses and email addresses turn into links automatically.