Barka da Zuwa
Shafin Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo
Wannan shafi mai albarka yana kawo masu abunda suka shafi al-amuran koyarwar addinin musulunci akan ingantacciyar fahimta ta Ahlussunnah.
- Read more about Barka da Zuwa
- 1707 views
drsaniumaroffice@gmail.com
Fassarar turanci na littafin
دراسات في حديث النبوي وتاريخ تدوينه
Idan ba a manta ba babban Malamin mu ya bada shawarar ina ma za a samu fassararsa da harshen turanci saboda da taimkon ƴan boko domin fuskantar ƙalubalen ake jefa wa hadisi da sunnar Annabi (SAW)
Jinkirin samun biyan bukatarka tare da naciyarka wajen addu'a kada ya zama sanadiyyar debe kaunarka. Allah ya laminta ne zai amsa maka addu'arka a kan abin da ya zaba maka, ba a kan abin da kai ka zaba wa kanka ba; a lokacin da shi ya ga dama, ba a lokacin da kai kake so ba".
Ibn Ata'illah As-Sikandari, shafi 19.
Neman Addu'a
Assalamu Alaikum Warhmatullah.
'Yan'uwana Musulmi,
1. Kasarmu tana cikin matsananciyar bukatar addu'o'inmu, saboda matsalar tsaro da ta ta'azzara, masu son su wargaza wannan Kasa sun fito haikan don cimma burinsu.
2. Al'ummarmu ta Musulmi a fadin Kasarnan suna bukatar addu'a, yadda matsalolinsu kullum suke ta karuwa, ake kwararar da jininsu a ko'ina ake salwantar da dukiyoyinsu, ake raba su da gidajensu da sana'o'insu.