Rana ta
[29]
Shekarar da ka rubuta
2019

Hikimar Allah Game Da Arzuki Da Talauci

1. Allah Ta'ala Yana cewa:
(Da kuma Allah Ya shimfida wa bayinsa arziki to da sun yi tsaurin kai a bayan kasa, sai dai kuma yana saukarwa ne daidai gwargwado yadda Ya ga dama. Lalle Shi Masani ne game da bayinsa Mai ganin (ayyukansu). [Shura, aya ta 27].

2. A wannan ayar Allah (SWT) ya bayyana hikimarsa ne wajen raba arzukinsa ga bayinsa yadda zai amfane su, ya tabbatar da cewa da zai yalwata wa kowa arzuki, ya ba wa kowa fiye da bukatarsa, to da yin haka ya haifar da barna a bayan kasa, domin mutane za su rika yi wa junansu dagawa da ji-ji-da-kai, babu mai sauraron wani. Sai dai Allah yana saukar da arzukinsa ne daidai gwargwadon yadda zai amfani mutane ba za su lalace ba gaba dayansu, ya ba wa wanda ya ga dama wadata, ya talauta wanda ya ga talaucin ya fi dacewa da shi, domin shi ne mai cikakken sanin halayen bayinsa mai ganin duk abin da suke ciki don haka yake gudanar da komai cikin hikima.