Rana ta
[26]
Shekarar da ka rubuta
2019

Guje wa mahallin Tuhuma

1. Wata rana Manzon Allah (SAW) yana i'itikafi a Masallacinsa a goman karshe na watan Ramadan, sai matarsa Ummuna Safiyya ta kawo masa ziyara da daddare. Bayan sun dan tattauna da shi sai ta tashi don koma wa gidanta. Manzon Allah (SAW) ya rako ta wajen kofar Masallaci. Suna tsaye tare sai wasu sahabbai biyu suka zo shigewa ta gabansu. Da suka gan su tsaye sai kunya ta kama su sai suka kara sauri. Da ganin haka sai Manzon Allah (SAW) ya ji tsoron kada Shaidan ya jefa musu wani mummunan zato a zukatansu na ganin Annabi (SAW) a tsaye tare da wata mace. Sai ya kira su ya shaida musu cewa, wannan Safiyya ce, watau matarsa ta aure ba wata bare ce suke tsaye tare da shi ba.

2. Wadannan sahabbai suka yi mamakin wannan magana da Manzon Allah (SAW) ya fada musu, domin kuwa ko da wasa ba za su taba munana wa Annabin Allah zato ba bayan sun yi imani da gaskiyarsa da nagartarsa. Amma duk da haka sai Manzon Allah (SAW) ya nuna musu cewa Shaidan yana gudu a jikin mutum a magudanar jini, watau ba ya raina duk wata irin dama da zai samu ta ganin ya saka masa mugun tunani a ransa, ko da kuwa ya san ba lalle ne ya yi nasara a kansa ba. [Dubi, Bukhari#2038 da Muslim#2178].

DARASI:

3. Don haka kamar yadda ya wajaba mutum ya kare kansa daga duk abin da zai zubar masa da mutunci, to hakanan ya zama wajibi ya kare mutuncinsa daga duk wani surutu na mutane da mugun zatonsu, domin daga zato ne sai a fara jin miyagun kalamai sun fara fitowa Idan kuma surutun mutane ya yi yawa game da mutuncin wani, to da wuya ne bai lalata masa shi ba, duk kuwa wanda ya yi asarar mutuncinsa to ya yi asarar kimarsa ne a idon jama'a, daga nan kuma ya yi asarar komai nasa a rayuwarsa. To don gudun irin wannan mummunan karshe ya zama wajibi a kiyaye mutunci tun daga farko.

4. Bai kamata mutum mai mutunci ba ya kai kansa inda zai jawo wa kansa zargi da tuhuma, ko da kuwa shi yana ganin kansa mai tsarki ne, ba ya da wata alaka ta kusa ko ta nesa da irin tuhumar da za a yi masa. Domin abin da zai yi la'akari da shi shi ne rayuwarsa a nan duniya ba tasa ce shi kadai ba, a'a tasa ce shi da 'yan'uwansa da masoyansa, idan har ya jefa kansa cikin zargi to ya tabka wa kansa da 'yan'uwansa da masoyansa babbar asara, ya jefa kansa da 'yan'uwansa cikin bala'i wanda zai cutar da addininsa da 'yan'uwansa Musulmi, musamman idan ya zamanto babban mutum ne wanda ake koyi da shi ko ake amfana da iliminsa, don haka zubewar mutuncinsa asara ce ga Musulmi da Musulunci baki daya.

5. Saboda haka duk sanda mutum ya tsinci kansa a inda yake tsoron za a yi masa mummunan zato, to ya yi maza ya bayyana wa mutane gaskiyar lamarin, kada ya dogara da cewa ai mutane suna ganin girmansa ba za su yi masa mummunan zato ba.