- 367 views
Sallar Juma'a Ga Matafiyi
1. Sallar Juma'a ba wajibi ce ba a kan matafiya. Idan matafiyi ya wuce ta wani gari ya samu su suna sallar Juma'a, yana iya bin su da niyyar sallar Azahar, domin ya samu sauraron huduba ya kuma rabauta da addu'ar 'yan'uwansa Musulmi.
2. Annabi (SAW) ya sallar Azahar a ranar juma'a a filin Arfa, ya kuma hada ta da sallar La'asar.
3. Sahabbai da yawancin tabai'ai musamman ma malaman Hijaz ba sa halartar sallar juma'a a yayin da suke cikin halin tafiya. Umar da Abdul-Aziz ya yi tafiya zuwa Halab, sai ya ce wa gwamnansa a garin: "Je ka yi wa mutane sallar juma'a, don mu matafiya ne". Watau bai fita zuwa sallar juma'a ba a ranar. [Dubi, Ibn Abi Shaibah#5105].
4. Yawancin Malamai suna ganin rashin halaccin kulla haramar tafiya ranar juma'a bayan rana ta yi zawali, ko bayan an kira sallar juma'a, domin a lokacin halartar sallar juma'a ta zama wajibi ga mutum, don haka dole ne ya tsaya a sallace ta tare da shi.
5. Babu wani hadisi da ya inganta a kan hana yin tafiya a ranar juma'a, kafin zawali ko bayan zawali. Duk abin da aka ruwaito daga Annabi (SAW) a kan haka bai inganta ba.
6. An samu wasu daga cikin magabata sun karhanta kulla haramar tafiya ranar juma'a sai bayan an yi salla, kamar Nana A'isha da Ibn Umar da Sa'idu dan Musayyab da Alkasim dan Muhammad. [Dubi, Ibn Abi Shaibah#5114 da 5115 da 5118, da Ibn Munzir, Al-Ausat#7139].
7. Sai dai kuma yawancin magabata suna ganin halaccin yin tafiya a safiyar ranar juma'a kafin zawali. Wannan ya tabbata daga Umar dan Khaddab, domin wata rana ya ga wani mutum sanye da tufafin matafiya yana haramar tafiya bayan an sauko daga sallar juma'a sai ya tambaye shi labarinsa, sai amasa masa da cewa, ai ya yi niyyar zai yi tafiya ne, to amma sai ya ji ba zai iya fita kama hanya ba ba tare da ya yi sallar juma'a ba, sai Umar ya cewa masa: "Juma'a ba ta hana yin tafiya matukar lokacinta bai shiga ba". [Abdurrazzak#5536].
8. Hakanan Abu Ubaidata ya fita tafiya ranar juma'a da safe bai jira sallar juma'a ba. [Dubi, Abdurrazzak #5538 da Ibn Abi Shaibah#5017].
Wannan shi ne abin da ya tabbata daga Al-asan Al-Basri da Ibnu Sirin da wasunsu.
[Dubi, Ibn Abi Shaibah#5109 da 5111].
9. Ibn Abi Shaibah da Abu Dawud sun ruwaito cewa wata rana Imamuz Zuhri ya yi haramar tafiya da safiyar ranar juma'a, sai aka masa magana a kan haka, sai ya ce: "Annabi (SAW) ya yi tafiya ranar juma'a". Dubi, Abu Dawud, Marasil#310 da Ibn Abi Shaibah#5113].