- 137 views
Gajeruwar Hanyar Rushe Musulunci
1. Mafi gajartar hanyar rushe addinin a jiya da yau ita ce rushe kima da darajar masu karantar da shi a idanun al'umma.
2. Tun da jimawa makiya Musulunci suka fahimci wannan. Don haka suka yi uwa da makarbiya wajen sukan masu dauke da karantarwar addinin Musulunci, kamar sahabbai da tabi'ai da manyan malamai, domin cim ma mummunar manufarsu.
3. Imamu Ahmad bn Hanbal yana cewa: "Idan ka ga mutum yana sukan sahabban Manzon Allah (SAW), to ka tuhumce shi da kin Musulunci". [Ibn Kasir, Al-Bidaya, juzu'i na 11, shafi 450].
4. Wannan dalili ne ya sanya makiya Musulunci suka rika sukan sahabbai, kamar Abu Huraira da Nana A'isha, domin rushe tarin ilimin da suka karbo daga Manzon Allah (SAW). Suke kuma sukan malaman tabi'ai, irin su Muhammad bn Shihab Az-Zuhri, domin lalata dimbin hadisan da ya ruwaito daga sahabbai.
5. A kullum masu kin su ga ci gaban addinin Musulunci fatansu shi ne su sami abin da za soki wani wanda ya yi fice cikin al'umma wajen yada karantarwar Musulunci domin su cire ganin kimarsa da mutuncin daga zukatan al'umma, su kuma haramta musu sauraron karantarwarsa da karuwa da fadakarwarsa.
6. Don haka duk masu kokarin bata sunan malamai su sani ba shi karankansa malamin suke kokarin rushewa ba, a'a suna sa'ayi ne don ganin sun rushe da'awarsa da karantarwarsa wadda gado ne na Annabi (SAW) a hannunsa. Allah ya ganar da mu. Amin..